20 Janairu 2026 - 09:59
Source: ABNA24
Iran: An Kama Shugabannin Tayar Da Tarzoma Guda 134

An kama kungiyoyin ta'addanci dake da alaka da Amurka da Isra'ila, cikin wannan aiki an kama wata tawaga mai mutane uku da ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Monarchist da wata tawaga mai mutane 5 da ke da alaka da kungiyar munafukai, kuma an kama nau'o'in bindigogi da bama-bamai daban-daban a yayin binciken maboyar wadannan mutane.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An kama jami'ai 134 masu jagorancin yan tarzoma da suke da alaƙa da kungiyar ta'addanci ta Amurka da sahyoniya a Lorestan 

Sifah Sayyid Abulfazl As sun sanar da ganowa da kama jami'an tarzoma 134 da manyan shugabanni masu alaka da kungiyar ta'addanci ta Amurka da sahyoniya a lardin Lorestan.

Sannan IRGC sun tarwatsa wasu kungiyoyin ta'addanci guda biyu na munafukai da masu neman mulki

 Sifah Imam Reza (AS) na Khorasan Razavi: tare da kokarin sojojin Imam Zaman a cikin kungiyar leken asiri ta IRGC na lardin Khorasan Razavi da makana leken asiri da haɗin gwiwar ɓangaren shari'a da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun gudanar da ayyukan bin diddigi da kai sumame wanda ya kai ga kamewa tare da tarwatsa wasu kungiyoyin ta'addanci dake da alaka da Amurka da Isra'ila, cikin wannan aiki an kama wata tawaga mai mutane uku da ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Monarchist da wata tawaga mai mutane 5 da ke da alaka da kungiyar munafukai, kuma an kama nau'o'in bindigogi da bama-bamai daban-daban a yayin binciken maboyar wadannan mutane.

Your Comment

You are replying to: .
captcha